10 Nuwamba 2026 - 22:07
Source: ABNA24
Hegseth Don Gujewa Tsige Shi: Iran Ce Ta Fara Yaƙin! Shure-Shure Baya Hana Mutuwa

Bayan ƙoƙarin da 'yan majalisar dokokin Amurka suka yi na takaita ikon soji na gwamnati da haɗarin tsigewa kan ministan yaƙi, Pete Hegseth ya yi gargaɗi cewa wannan ƙuduri yana aika wa maƙiyan Amurka ciki har da Iran saƙon rauni.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: "Pete Hegseth", ministan yaƙin Amurka, a martaninsa ga wani ƙuduri kan takaita ikon gwamnatin wannan ƙasar wajen gudanar da ayyukan soji, ya ce a tarihin Amurka babu wani ministan yaƙi da aka kore shi a lokacin gudanar da wani aikin soji.

Tare da sukar ƙudurin da ke takaita ikon soji na gwamnatin Amurka da tsoron tsige shi ya bayyana cewa: "Wannan ƙuduri yana aika wa maƙiyanmu, ciki har da Iran, cartels da sauran maƙiya, saƙon cewa Amurka za ta hukunta mayaƙanta da shugabanninta na fararen hula saboda gudanar da ayyukan soji na doka cikin nasara."

Ministan yaƙin gwamnatin ta'addanci ta Amurka a ci gaba da jawabinsa a taron manema labarai ya yi ƙarya ya ce: mu ba mu fara wannan yaƙin ba; Iran ce ta fara shi shekaru 47 da suka gabata.

Ministan yaƙin Amurka ya kuma ce tarihi zai yi hukunci kan yaƙin da Iran wanda ya bambanta da abin da aka yi imani da shi a yau.

Hegseth a wani ɓangare na sambatunsa ya nanata cewa Washington za ta sa ido kan halin cikin Iran daga kusa da kuma a matakai daban-daban.

...............

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha